Kano ta dauki matakan gaggawa kan Ebola

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mutane bakwai ne aka tabbatar sun kamu da ebola a Najeriya, a cikinsu wata 'yar kasar da kuma dan Liberia sun mutu

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da wani kwamiti kan cutar Ebola a karkashin jagorancin Daraktan kula da lafiyar al'umma na jihar, Dr. Nasir Mahmud.

Hakan dai wani bangare ne na matakan gaggawa da jihar Kano ke dauka game da cutar ebola da ta bulla a Najeriya.

A cikin wani jawabi na musammam ta kafofin yada labarai, gwamnan jihar Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce gwamnati ta yi cikakken shiri ko da za a samu barkewar cutar a Kano.

Ya ce ma'aikatan lafiya suna cikin shirin ko-ta-kwana domin tunkarar bullar kwayar cutar a jihar da ta fi kowace yawan al'umma a kasar.

Gwamnan ya ce a yanzu sun tanadi kayayyaki kare-kai na jami'an lafiya guda 33, an kuma samar da motar daukar marasa lafiya don ko-ta-kwana tare da ware wani yanki da za a kwantar da mutanen da suka kamu da cutar ta Ebola.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba