Nigeria ta ayyana dokar ta-baci kan Ebola

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wadanda suka harbu da cutar duka ma'aikatan jinya ne da suka kula da dan Liberiya, Patrick Sawyer

Gwamnatin Najeriya ta ayyana dokar ta-baci a kan cutar Ebola da ta bulla a kasar bayan mutuwar 'yar kasar ta farko.

Ministan lafiya na kasar, Farfesa Onyenbuchi Chukwu ne ya bayyana hakan bayan kammala taron mako-mako na majalisar ministocin kasar a Abuja a ranar Laraba.

Ya ce wata cibiyar daukar matakan gaggawa na hana bazuwar cutar ta ebola za ta fara aiki a Lagos din daga ranar Alhamis ba dare ba rana.

Mutane a Najeriyar, musamman mazauna jihar ta Lagos na ci gaba da nuna fargaba game da bullar cutar a sanadiyyar wani dan Liberiya da ya kawo cutar kasar a watan Yuli.