Sojin Nigeria sun fafata da 'yan Boko Haram

Dakarun sojin Nigeria
Image caption Rahotanni sun ce wasu mutanen kauyukan da aka fafata sun tsere zuwa kan tsaunuka da cikin daji.

Rundunar sojan Nijeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar fatattakar 'yan kungiyar Boko Haram da suka addabi mazauna kauyukan Delwa da Mustafari da Manga da Wanga da kuma garin Damboa na jihar Borno.

A wata sanarwa, rundunar ta ce sojojinta na ci gaba da yunkurin ganin sun fatattaki maharan da suka auka wa garin Gwoza tun a ranar Talata, inda aka kashe mutane da dama.

Kawo yanzu dai babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin sanarwar da dakarun sojan Nijeriyar ta fitar.

Rahotanni na baya-bayan nan sun ce akwai gawawwakin mutanen da aka kashe ba tare da an yi musu jana'iza ba, saboda akasarin mutanen garin sun tsere zuwa kan tsaunuka da cikin daji.