Shugaba Jonathan ya kira taron gaggawa kan Ebola

Shugaban Nigeria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Nigeria da dama na ci gaba da fargabar yaduwar cutar Ebola a kasar.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kira taron gaggawa kan cutar Ebola yayin da 'yan kasar ke ci gaba da fargabar yaduwar cutar a kasar.

Kakakin shugaban kasar Rueben Abati ya ce shugaba Jonathan ya soke wata ziyarar da ya shirya kai wa zuwa Owerri dake kudu maso gabashin Nigeria don tattaunawa kan yadda za'a shawo kan wannan cutar.

Wannan taron da shugaban Nigeria ya kira ya biyo bayan wani taro ne Jami'an gwamnatin kasar suka yi ranar Alhamis da dukkanin Jakadu da jami'an diflomasiyyar da ke kasar domin sanar da su halin da ake ciki game da bullar cutar Ebola a kasar.

Ana yi wa taron kallon wani mataki na kwantar da hankalin al'ummar kasashen waje da ke Najeriyar.