Me ake yi da tsofaffin wayoyin salula a Afrika?

Hakkin mallakar hoto AFP

Wani nazari da masana suka yi ya nuna cewa nahiyar Afrika ce ta fi yawan masu wayoyin salula a duniya, inda adadinsu ya kai miliyan 500.

A kowace shekara yawan masu wayoyin salular na karuwa da kashi 20 cikin 100 a tsawon shekaru biyar da suka gabata.

Sai dai abin tambaya a nan shi ne, me 'yan Afrikan ke yi da wayoyin salularsu idan sun tsufa ko sun lalace ?

Wasu masu wayoyin salular sun bayyana wa BBC cewa idan wayoyin sun tsufa su kan ba da su kyauta ga 'yan uwa da abokan arziki masu karamin karfi.

Haka kuma wata hanya ta rabuwa da tsofaffin wayoyin salular ita ce ta kai wa wasu wurare da aka tanada domin tattara lalatattu ko tsofaffin wayoyin salula.

A kasashe irin su Nijar da Burkina Faso da Benin da Madagascar da kuma Ivory Coast, kamfanin wayoyin salula na Oranj (Orange) ya fito da wani shiri na tattara tsofaffin wayoyin salular.

Kamfanin kan bayar da lada ga masu gyaran wayoyin salula ko masu sayar da wayoyin, wadanda ke tattara tsofaffi da kuma lalatattun wayoyin salula.

Ana kai tsofaffin wayoyin kasar Faransa, inda ake sake sarrafa su, kafin daga bisani a sake maido da su kasuwannin Afrika.