An kashe mutane akalla 10 a Kamaru

Mayakan kungiyar Boko Haram Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan kungiyar Boko Haram

Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai wa wani gari a arewacin Jamhuriyar Kamaru hari, inda suka kashe mutane akalla goma.

Maharan sun afkawa kauyen Zigague da ke arewacin Kamaru da tsakar rana a kan babura a ranar Laraba .

Sun kuma kai wa gidan dagaci da kuma wani caji ofis din 'yan sanda hari.

Haka kuma sun yi musayar wuta da sojojin Kamaru inda aka kashe sojan kamaru daya da kuma fararen hula tara.

Kasashen Kamaru da Najeriya da Chadi da kuma Nijar sun amince su kafa dakarun kawance da za su yi yaki da 'yan kungiyar Boko haram.