Tallar tufafi ta intanet

Image caption Tallata tufafin kawa a dandalin sada zumunta ya kawo sauyi a fannin zayyana

Masu zayyana tufafi daga Afrika, za su tallata ayyukansu a kasuwar baje kolin tufafi ta wannan shekara da za a yi a London.

Ana sa ran wannan taro na mako daya, zai nuna irin fasahar da masu yin tufafin kawa daga nahiyar Afrika ke da ita, a taron da za a yi a karo na hudu.

A cewar Josette Matomby, wata 'yar asalin kasar Congo da ta yi fice a fannin zayyana tufafi wacce kuma ke zaune a gabashin London, nahiyar Afrika ta zama abin alfahari a wannan fanni.

Ta kara da cewa hakan ya sa fitattun masu zayyanar tufafi a duniya irinsu Burberry ke danganta kansu da tufafin da suka samo asali daga nahiyar ta Afrika.

Daga cikin dalilan shirya wannan taro, wanda ake yin shi a shekara-shekara, akwai batun cewa kwararrun na Afrika ba sa cin moriyar ayyukansu.

Sai dai taron zai gudana ne, a dai dai lokacin da wasu ke cewa, wadanda suka fi amfana da fannin yin tufafi a Afrika, su ne wadanda ke nuna kwarewarsu ta dandalin sada zumunta irin su Twitter da YouTube da makamantansu.

Image caption Intanet ta daukaka al'adun Afrika

Hakan a cewar masu irin wannan tunani, yana bai wa madinkan damar nuna fasaharsu ga sassan duniya musamman ma matasa.

Kadan daga cikin ire ire wadannan fitattun masu yin tufafi, akwai Shirley B. Eniang, wacce ke zaune a London amma 'yar asalin Ghana da Nigeria.

Shirley na yada fasahar ta dinki ga akalla mutane dubu 500 wadanda ke ziyartar shafinta na YouTube.

Har ila yau akwai Oghosa Ovienrioba, haifaffiyar Birtaniya 'yar shekaru 22 da ke da asali da Nigeria.