Yarjejeniyar dakatar da bude wuta ta gamu da cikas

Gaza Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata roka da aka harbo daga Zirin Gaza

Yarjejeniyar dakatar da bude wuta tsakanin Israila da Kungiyar Hamas a zirin Gaza ta gamu da cikas .

Rahotani sun ce bagarorin biyu sun kasa cimma matsaya a yukurin sabunta yarjejeniyar.

Wani mai magana da yawun Hamas ya yi kira ga wakilan Palasdinawa da ke halartar zaman sasanta rikicin a Alkahira, da kada su amince da tsawaita yarjejeniyar idan Isra'ela ba ta amince da bukatunta ba.

Kungiyar Hamas ta nemi Israila akan bude hanyoyin Gaza da ta rufe .

Wata kafar talibijin a Israila ta ce an harba rokoki daga Zirin Gaza zuwa wani gari dake kudancin kasar.