Amurka zata ba Nijeriya miliyoyin Abatcha

Marigayi Janar Sani Abatcha,  tsohon shugaban Nijeriya Hakkin mallakar hoto nigeria at 50
Image caption Marigayi Janar Sani Abatcha, tsohon shugaban Nijeriya

Ma'aikatar Shari'a ta Amurka ta ce ta yi nasarar samun iko da kusan dala miliyan dari biyar da tsohon shugaban Nijeriya, Janar Sani Abatcha da mukarrabansa suka boye a kasashen Turai.

A wata sanarwa, mataimakiyar Antoni Janar Lelie Caldwell, ta ce Janar Abatcha yayi amfani da mukaminsa wajen wawure miliyoyin daloli , ta hanyar sata ba ji,ba gani.

An boye kudin ne a asusun ajiya a Birtaniya, da Jersey, da kuma Faransa.

Ma'aikatar Shari'ar ta ce za a mayar da kudin ga Nijeriya.

Janar Abatcha ya mulki Nijeriya ne har zuwa lokacin da ya rasu a 1998.