Ebola: WHO ta ayyana dokar ta-baci

Hakkin mallakar hoto n
Image caption Kawo yanzu ba a samu maganin cutar ta Ebola wadda ta hallaka mutane sama da 900 a Yammacin Africa ba

Hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta ayyana bazuwar cutar Ebola a Afrika ta Yamma a matsayin lamarin da ke bukatar matakin gaggawa na kasa da kasa.

Kungiyar ta fitar da wannan sanarwa ne bayan taron kwanaki biyu da ta yi a Geneva.

A taron ta tabbatar da cewa yanayin cutar ta Ebola a yankin Afrika ta Yamma babbar barazana ce kuma hadari ne ga sauran kasashe.

Hukumar ta kuma gabatar da shawarwarin da za a bi domin yaki da cutar a kasashen da ta bulla.

Shawarwari

Hukumar lafiya ta duniya ta bukaci Shugaban kowace kasa, ya ayyana dokar ta-baci, da gabatar da jawabi da kansa, inda zai bayar da bayanai kan matakan da ake dauka da kuma yadda jama'a za su ba da gudummawarsu na hana bazuwarta.

Kasashe su farfado da cibiyoyinsu na bayar da kulawar gaggawa ta lafiya da kuma tafiyar da aiki tare tsakanin dukkanin hukumomi da kungiyoyi masu nasaba da yaki da cutar.

Kasashe su tabbatar da sun shigar da shugabannin jama'a, na addini da gargajiya da sauransu domin kowa ya taka rawa wajen yakin, ta hanyar gano mai alamun cutar, don ba shi kulawar gaggawa.

Hakkin mallakar hoto AP

Kasahe su tabbatar sun samar da cibiyoyin tantance masu fita daga kasar a filayen jirgin sama da tashoshin jiragen ruwa da iyakoki na kasa.

Hukumar ta kuma bayar da shawarar hana tafiye-tafiye zuwa kasashen da cutar ta bulla, indai ba na ma'aikatan lafiya ba domin yaki da cutar.

Hukumomin gwamnati su tabbatar kwararru ne ke aikin binne gawa, amma da tanadin al'ada da kuma na 'yan uwa.

Kasashen da babu ebola

Su kuma kasashen da cutar ba ta bulla ba, hukumar ta duniya ta shawarce su da su dauki matakan da suka hada da;

Kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana na hana shigowa da kuma yada cutar.

Hukumomi su rika bai wa jama'a cikakkun bayanai kan kauce wa kamuwa da cutar da bazata.

Gwamnati ta bai wa masu tafiye-tafiye zuwa kasashen da ke da hadarin cutar cikakkun bayanai kan hadarin annobar.

Karin bayani