Ebola:Kamaru ta karfafa bincike akan iyakokinta

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasashe daban daban na tantance matafiya don takaita yaduwar cutar Ebola

Gwamnatin Kamaru na kara karfafa matakan bincike akan iyakokin ta da wasu kasashe domin hana yaduwar cutar Ebola a kasar.

Haka kuma gwamnatin kasar ta ware wasu asibitoci don tantance lafiyar wadanda suka shigo cikin kasar daga kasashen da cutar ta yi kamari.

Rahotanni sun ce gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta taimaka wa Kamaru da wasu kayayyaki na kariya wajen kamuwa da cutar ga jamiā€™an kiwon lafiya.

Yanzu haka dai kasashe daban daban na daukar matakai don takaita yaduwar cutar Ebola wacce kawo yanzu ta hallaka fiye da mutane 900 a Yammacin Afrika.