Sabuwar dokor shafin Sada Zumuntar China

Manhajar sada zumunta ta Wechat Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu suka na ganin sabuwar dokar yin rijistar sunan asali hanya ce ta hana mutane tofa albarkacin bakinsu.

A karkashin sabuwar dokar da kasar China ta fitar, masu amfani da shafukan sada zumunta ya zama wajibi su yi rijistar ainahin sunan su, tare da samun izini kafin su wallafa wani labari da ya shafi siyasa.

Mutanen da suke amfani da dandalin Wechat su ma sai sun amince da wasu sharudda kafin su wallafa wani abu a shafin su, kamar yadda kafar yada labaran kasai ta bayyana.

Hakan dai ya biyo baya ne sakamakon bayanin da jami'an kasar Korea ta Kudu suka fada na cewa an toshe kafar sada zumunta na kasashen ketare irinsu Kakao Talk da kuma Line.

Shekaru biyu da suka gabata dai kasar ta China ta sanya matakai kwatankwacin wannan akan.

Haka kuma akwai matakan tsaro sosai akan yanar gizon China, inda aka taba rufe shafukan sada zumunta irinsu Facebook da Twitter.

A bangare guda kuma daruruwan miliyoyin mutane ne ke amfani da shafukan na sada zumunta na kasar ta Sin.

Gargadi.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Ofishin hukumar da ke sa ido akan shafukan internet SIIO ne dai ya fitar da sanarwar da ta fara aiki nan take a ranar alhamis kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya rawaito.

Dokokin za su yi aiki ne akan shafukan da ake amfani da su wajen watsa labarai ga masu hulda da shafukan.

Sanarwar ta ce Shafukan aika sakonnin kar ta kwana na sada zumunta za su bukaci sunayen masu amfani da shafin na asali da kuma wasu bayanai game da su kafin ma a yi musu rijistar.

Idan kuma masu amfani da shafukan su ka yi rijista, sai kuma su rattaba hannu kan amincewa da amfani da dokokin da aka shinfida musu da suka hadar da kare muradun al'umma da wallafa sahihan labarai.

Shafin sada zumunta na Tencent wanda shi ne mamallakin shafin Wechat kuma yana daya daga cikin wadanda suka goyi bayan wannan batu, ya bayyana cewa manufar wadannan sabbin dokokin shi ne domin hana yaduwar labaran da ka iya cutar da jama'a da kuma jita-jita.

A dan haka ofishin SIIO ya bukaci al'umma da su yi biyayya ga wannan doka.

Sai dai masu suka akan lamari na ganin cewa, batun yin rijista da sunan mutum na asali wani yunkuri ne na hana mutane tofa albarkacin bakinsu game da gwamnatin kasar ta Sin, ka na kuma a bangare guda hukumomi ba za su sha wahalar cafke mutanen da suka wallafa irin wadannan batutuwa a shafin sada zumunta ba.