Amurka ta kai hari kan ayari na 'yan jihadi

Harin Amurka kan 'yan jihadi a Iraqi
Image caption Harin Amurka kan 'yan jihadi a Iraqi

Amurka ta yi karin bayani game da hare-haren da take kaiwa ta sama a kan mayaka 'yan kishin Islama a Iraqi - tana cewar a farmakin baya-bayan nan ta lalata wani ayarin mayaka da tace yana barazana ga birnin Irbil dake yankin arewacin kasar.

An lalata ayarin. Bugu da kari kuma akwai alamun wasu kayan agaji sun isa ga mutanen Yazidi,dubban mabiya wasu addinai 'yan tsiraru da suka tsere daga gidajensu.

Fadar gwamnatin Amurkar dai ba ta ambaci tsawon lokacin da za a dauka ana kai farmakin ba. Tana bukatar ganin hukumomin Iraqin sun kara yunkuri wajen fuskantar mayakan 'yan Jihadi.

Har ila yau kuma Amurkar tana kara matsa lamba a kan 'yan siyasa na Iraqin su kafa gwamnatin hadin-kan kasa wadda za ta iya fuskantar barazanar masu jihadin.

Karin bayani