Ebola: Nigeria na daukar matakan kariya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Gwamnatin Nigeria ta ce zata ci gaba da daukar matakai don ganin an takaita yaduwar cutar a kasar.

Hukumomin Nigeria na aiwatar da sabbin matakan hana yaduwar cutar Ebola bayan da shugaba kasar, Dr Goodluck Jonathan ya ce cutar wata babbar matsala ce da ke bukatar matakan gaggawa.

Wasu daga cikin matakan da kasar ke dauka sun hada da kafa sansanoni na musamman don kebe wadanda suka kamu da cutar da kuma tantance matafiya da ke shigowa da kuma fita daga kasar.

Baya ga ayyana dokar ta baci kan cutar Ebola, shugaban Nigeria ya amince da ware Naira biliyan daya da miliyan dari tara don daukar matakan hana yaduwar cutar a kasar.

Shugaba Jonathan ya kuma yi kira ga gwamnatocin jihohin kasar da makarantu masu zaman kansu da su duba yiwuwar kara hutun da dalibai ke yi a halin yanzu har sai bayan an tabbatar da cewa an kawar da barazanar da cutar ke yi a Nigeria.