Obama: Zamu ci gaba da kai hari kan ISIS

Shugaba Obama Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Obama

Shugaban Amurka Barack Obama ya ce idan ta kama, rundunar sojin kasarsa, zata ci gaba da kai hari a kan mayakan sunni a arewacin Iraki.

Amma ya ce tsayayyar gwamnatin hadaka, ita ce kawai zata iya ganin bayan mayakan na ISIS.

Don haka ya bukaci jama'ar Irakin da su hada kansu don yakar wadanda ya kira 'yan ta'adda, saboda 'yan kasar su samu kyakkawar makoma.

Shugaba Obama ya kuma ce kasarsa zata cigaba da yunkurin taimaka wa dubban mabiya addinin Yazidi da suka rasa na yi, a tsaunukan arewacin kasar.

Ya kuma kara da cewa ya yi magana da shugaban Faransa da Praministan Birtaniya, kuma duk sun tabbatar masa da cewa zasu taimaka wajen kai agajin gaggawa.