Shugaban kungiyar likitocin Najeriya ya yi murabus.

Doctors Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Doctors

Shugaban kungiyar likitoci a Najeriya Dr. Kayode Obembe ya yi murabus bayan samun rarrabawar kai a tsakanin 'ya'yan kungiyar sakamakon janye yajin aiki da suke yi.

A cikin wasikar da ya bayar ta murabus din na sa a jiya Juma'a, ya ce ya yi murabus din ne kasancewar wani bangare na kungiyar ta su ya ce zai cigaba da yajin aiki.

A ranar larabar data gabata ne shugaban kungiyar ya fito ya bayar da sanarwar cewa sun dakatar da yajin aikin da suka shafe kwanaki suna yi saboda saboda barkewar cutar Ebola a kasar da kuma saboda mutanen da ake ci gaba da jikkatawa sakamakon hare-haren Boko Haram a kasar su samu kulawar likitoci.

Sai dai wasu 'ya'yan kungiyar da kuma wasu shugabannin kungiyar na jihohi sun ce shugaban na kasa ya yi gaban kansa ne kawai.

Likitocin dai sun kwashe fiye da wata guda suna yajin aiki abin da ya janyo damuwa ga wasu 'yan kasar ganin cutar ebolar ta bulla a lokacin da ake bukatarsu a bakin aiki.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba