Ebola ta yi tsanani a Liberia inji MSF

Kungiyar Agaji ta Medecins Sans Frontiers tace cutar Ebola ta dabaibaye ma'aikatar kiwon lafiyan Liberia.

Wata jami'ar kungiyar na ganin cewa ma'aikatar bata dauka barkewar cutar tayi tsananin da tayi ba.

Ta ce "Manyan asibitocin Manrovia biyar sun kasance a rufe yau fiye da mako guda. Koda yake wassun su sun fara aiki, amma akwai wasu asibitocin da ma'aikatan su suka kaurace masu."

A jiya asabar, 'yan sanda sun tarwatsa gungun wasu mutane dake zangar-zangar nuna bakin cikin su akan yadda gwamnatin kasar ke bullowa cutar.

Yanzu haka cutar na addabar wasu kasashe a yammacin Afrika.

Najeriya ta ayyana dokar tabaci akan cutar.

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya amince da ware Naira biliyan daya da miliyan dari tara don daukar matakan hana yaduwar cutar a kasar.

Shugaba Jonathan ya kuma yi kira ga gwamnatocin jihohin kasar da makarantu masu zaman kansu da su duba yiwuwar kara hutun da dalibai ke yi a halin yanzu har sai bayan an tabbatar da cewa an kawar da barazanar da cutar ke yi a Nigeria.

Hukumar lafiya ta duniya ta ayyana dokar ta-baci a kan cutar ta Ebola bayan cutar ta kashe kusan mutane 1000 tare da shafar wasu fiye da 1000 a yammacin Afrika.