Wakilan Falasdinawa za su fuce daga Sulhu

Wata mata a Gaza na kuka Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kashe mata da kananan yara a rikicin da aka faro shi tun 8 ga watan Yuli.

Wakilan Falasdinawa sun fara barazanar ficewa daga tattaunawar sulhu da aka shirya yi a birnin Alkhahira na kasar Masar, matukar wakilan Isra'ila ba su zo ba, inda ake sanya ran za a ci gaba da tattaunawa a yau lahadi.

Sai dai Isra'ila ta ce za a yi tattaunawar ce kawai idan Hamas ta daina harba mata makaman Roka, yayin da Falasdinawa ke cewa Isra'ila ta daina gindaya sharuddai irin wannan.

Yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Falasdinawa ta kwanaki uku ta zo karshe tun a shekaran jiya juma'a, kuma tun a wannan lokaci Isra'ila ta ci gaba da yi wa Gaza luguden wuta ta sama, ya yin da ita ma Hamas ta ci gaba da mai da martani da harba makaman roka.

A bangare guda kuma Amurka da Faransa da Burtaniya sun yi kira ga bangarorin biyu su shiga tattaunawa sulhu don kawo karshen rikicin.