Jirgi ya fadi a Iran

Hakkin mallakar hoto Hadi

Wani jirgin sama ya fa fadi a wata unguwa a Tehran, babban birinin Iran.

Yawancin mutane 48 dake jirgin sun riga mu gidan gaskiya.

An ruwaito cewa Jirgin na kan hanyar sa ce ta zuwa garin Tabas a gabashin kasar

Hassan Molla wani ganau ne kuma ya ce "kwatsam sai naga jirgi ya na duri zai sauka a kaina sai nayi maza na tsaida babur dina na yi kasa."

Ana dora alhakin hadurran jiragen saman da suka faru a baya a kasar akan tsoffin jirage da basa samun gyara.

Takunkumin da ksashen yammacin duniya suka sawa kasar yasa bata iya sayen sabbin jirage ko shigo da kayan gyara.