An kai ma 'yan Yazidi agaji a Iraki

Mabiya addinin Yazidi a Iraki Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mabiya addinin Yazidi a Iraki

Jiragen Amurka da na Birtaniya sun saukar da kayan agaji ga dubban jama'ar da hare-haren mayakan ISIS suka rutsa da su a tsaunukan arewacin Iraqi.

Wani kakakin ma'aikatar tsaro ta Pentagon ya ce cikin kayan agajin da aka saukar wa mabiya addinin Yazidi, har da dubban galan-galan na ruwan sha, da kuma abincin gwangwani.

A jiya ne shugaba Obama ya sha alwashin taimakawa 'yan Irakin ta hanyar kai hare hare ta sama a kan mayakan ISIS , wadanda suka yi wa mabiya adinin Yazidin 'yan tsiraru, kawanya a wani tsauni.