Cutar amai da gudawa a Ibi - Dokar ta baci

Cutar amai da gudawa a Nijeriya
Image caption Cutar amai da gudawa a Nijeriya

Mazauna garin Ibi dake cikin jihar Taraba a Nijeriya sun shiga mako na biyu cikin dokar hana fita ba-dare-ba-rana, wadda hukumomi suka kafa domin shawo kan bazuwar tarzoma mai nasaba da kabilanci da addini.

Rahotanni dai na bayyana cewa jama'ar garin na ci gaba shan ukuba saboda dokar, inda har aka samu barkewar cutar amai da gudawa.

Mutane a kalla 15 ne ciki har da jami'an tsaro biyu suka mutu sakamakon dokar ta-bacin.

Mutanen garin dake kokawa da tsawon lokacin da aka shafe ana aiki da dokar sun ce suna fuskantar ukubar yunwa da kishin-ruwa, abinda ke tilasta musu shan gurbataccen ruwa.

Karin bayani