Gwajin kan maganin cutar Ebola

Hakkin mallakar hoto AFP

Anya ana iya gudanar da binciken da ya dace akan ingancin magani a lokacin da ake tsakiyar annoba?

Yayin da kwararru kan harkar kiwon lafiya ke kokarin samun amsar wannan tambayar, Najeriya ta isa misali kan sarkakiyar da ka iya biyo bayan gwajin magani.

A shekarar 1996 kamfanin harhada magunguna na Pfizer wanda ke da mazauninsa a Amurka ya gudanar da gwaji a lokacin tsakiyar annobar sankarau. Mutane kimanin 12,000 suka rasu cikin watanni shida a sakamakon cutar a jihar Kano dake arewacin kasar.

Kawo yanzu babu wani tabbaci da aka samu kan maganin ebola.

Tasirin da illar gwaji zai yi idan aka sami kuskure yana iya daukar shekaru masu yawa.

Hasali dai gwajin Trovan ya kara sanya shakku kan maganin bature da kuma haifar da nakasu ga kokarin yin allurar rigakafi ga kananan yara a arewacin Najeriya.

Karin bayani