Kokarin samo maganin cutar Ebola

Hakkin mallakar hoto No credit
Image caption Har yanzu ba'a samu magani ko rigakafin cutar Ebola ba

Hukumar lafiya ta duniya WHO za ta gudanar da wani taro da ya hada da kwararrun jami'an kiwon lafiya a Geneva domin sake binciken amfani da magungunan gwaji ga wadanda suka kamu da cutar Ebola.

Za su duba yiwuwar yin amfani da magungunan da ba a taba gwada su ga dan adam tare da samar da irin wadannan magunguna da kuma yadda za a yi amfani da su.

An bai wa wasu 'yan asalin Amurka da suka kamu da cutar ta Ebola irin wannan magani, kuma rahotanni sun ce bayan amfani da maganin suna samun sauki.

Kawo yanzu dai babu takamamman magani ko rigakafin cutar ta Ebola mai saurin hallaka dan adam.