Shugaban Iraqi ya bukaci kafa gwamnati

Shugaban kasar Iraqi Fuad Masum Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban kasar Iraqi Fuad Masum

Shugaban Iraqi, Fuad Masoum, ya nemi mutumin da jama'iyun yan Shi'a a majalisar dokoki suka nada da ya kafa gwamnati.

Mutumin da yan majalisar suka nada shi ne Haidr al-Abadi, mataimakin kakakin majalisar dokokin.

Ta hanyar nada Haider al-Abadi a matsayin Pirayim Minista, bangaren yan shi'a, na kwancen kasa, ya kalubalanci Pirayim Ministan wucin gadi, Nouri al-Maliki, wanda ya bayyana karara yana neman wa'adin iko karo na uku.

A jiya lahadi Nouri al-Maliki yayi barazanar kai Shugaban kotu, bayan da ya zarge shi da gaza cimma wa'adin nada wani sabon Pirayim Minista domin dalilai na siyasa.

Karin bayani