Iraki: an nemi a maye gurbin Al-Maliki

Shugaban kasar Iraki ya nemi mataimakin kakakin majalisar dokokin kasar da ya maye gurbin Nouri al-Maliki a matsayin Fryminista.

Nouri al-Maliki ya bayyana karara cewar yana son wa'adin iko karo na ukku, to amma manyan jama'iyun 'yan Shi'a sun zabi Haider al-Abadi a maimakonsa.

Daga baya Haider Al-Abadi ya bukaci yan Iraqi su hada kai a yaki da kungiyar yan gwagwarmaya, ta kasar musulunci.

To amma Nouri al-Maliki ya bayyana zaben Haider Al - Abadi a matsayin wani saba tsarin mulki mai hadari.

Tun farko kakakin jama'iyar Noura al-Maliki ta Dah'wa, Khalaf Abdul Samad ya karanta sanarwar yin wasti da zabin a madadinsa ta gidan.

Amurka ta yi alkawarin bayar da goyon baya ga Haider Al -Abadi, wanda Sakatare Janar na MDD Ban Ki-Moon yayi marhabin da zabin nasa.