Al'ummomi sun fara taron wayar da kai

Yaki da cutar Ebola Nijeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yaki da cutar Ebola Nijeriya

A Najeriya Yayinda gwamnatin Kasar ta ayyana dokar ta-baci a kan cutar nan ta Ebola mai kisa, a jiya al'ummar musulmi a Abuja suka shirya gudanar da wata lakca domin wayar da al'umma kai game da cutar.

Babban jami'in kiwon lafiyar nan dake cibiyar hana yaduwar cututuka a kasar, Dr Nasir Sani Gworzo tare da wasu kwararru ta bangaren kiwon lafiya, na daga cikin wadanda suka halarci wurin taron.

Dr Gwarzon ya bayyana alamomin cutar ta Ebola. Tare da kira ga jama'a su kare kansu daga kamuwa da cutar.

Dr Sani Gwarzo ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewar wanka da shan ruwan gishiri sune maganin cutar.

Karin bayani