Mata ne ke binne gawarwaki a Gwoza

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Yan Boko Haram sun kafa tutoci a fadar Sarkin Gwoza.

Rahotannin da ke fitowa daga garin Gwoza na jihar Borno da ke arewacin Nijeriya na cewa matan da 'yan Boko Haram suka kashe musu mazaje ne ke jana'izar mamatan su.

Wani dan majalisar wakilai Hon Peter Biye, ya shaidawa BBC cewa akai gawarwakin mutane da dama zube a kan titunan garin ba tare da an binne su ba saboda matan sun yi bakin kokarin su wajen jana'izar gawarwaki har sun gaji.

'Ya ce ya zuwa yanzu babu wani namiji maji karfi a garin Gwoza, ko dai an hallaka su yayin da wasu kuma suka tsere zuwa kan tsaunuka.'

Yanzu haka dai 'yan kungiyar Boko Haram sun nada Amir da ke gudanar da al'amuran shari'a, tare da kafa tutoci a muhimman wurare da suka hadar da gidan gwamnati da fadar Sarkin Gwoza.