Dakarun Nigeria sun musanta rahoton Amnesty

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Amnesty na zargin sojojin Najeriya da cin zarafin wasu mutane a arewacin kasar.

Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da rahotan da kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta fitar kan zargin sojojin kasar da aikata laifuffuka cin zarafin bil'adama.

Kungiyar ta Amnesty ta fitar da wani fai-fan bidiyo da ke nuna yadda wasu sanye da khakin sojojin Najeriyar na cin zarafin wasu mutane a arewacin kasar.

Sai dai wata wasika ta hukumar tsaron Nigeria ta ONSA ta ce, Amnesty ta himmatu ne wajen ganin ta yada labarai ba tare da ta jira an yanke hukunci ba.

Gwamnatin ta kara da cewa kamata ya yi kungiyar ta tsaya ta yi nazarin yadda lamarin ya ke kafin ta fitar da rahoton ta.