Matan sojojin sun yi zanga zanga a Borno

Sojojin Nigeria

Rahotanni daga jihar Borno da ke arewacin Nigeria sun ce matan sojoji da yara da ke barikin sojoji na Giwa a Maiduguri sun gudanar da zanga-zanga domin hana kai mazajen su fagen daga.

Wasu daga cikin matan sun shaidawa BBC cewa sun gaji da mayar da su zaurawa da marayu sakamakon irin yadda ake hallaka sojoji a dauki ba dadin da ake yi da 'Yan Boko Haram.

Matan sun yi zargin cewa mazajen su ba su da cikakkun kayan aikin da za su iya fafatawa da 'yan Boko Haram.

Sun kuma bayanna cewa ba za su taba bari mazajen su fita ko kofar gida ba, ballantana su bar barikin.

Rahotanni sun ce a makon daya gabata an kashe sojojin Najeriyar da dama a artabun da aka yi da 'yan Boko Haram a garin Gwoza.