Ebola: WHO ta nemi a binciki matafiya

Jami'an lafiya ma'aikatan ciwon Ebola Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'an lafiya ma'aikatan ciwon Ebola

Hukumar lafiya ta duniya - WHO, ta bukaci kasashen da aka samu bullar cutar Ebola a cikinsu da su binciki dukanin matafiyan dake barin kasashen don gano alamomin cutar.

Ta ce dole ne a samu wuraren bincike a manyan filayen jiragen sama da tashoshin ruwa da kuma manyan wuraren fita daga kasashen ta kasa, tare da hana duk wani da ya nuna alamomin yana dauke da cutar daga tafiya.

A halin yanzu kasar Kamaru ta rufe kan iyalolkinta na kasa da ruwa da kuma ta sama tare da Najeriya a wani kokari na taimakawa ga dakile watsa cutar ta Ebola.

Cutar dai ta kashe mutane fiye da dubu daya a yammacin Afrika, tare da mutuwar wasu mutanen a Najeriya.

Wani Ministan Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, ya ce riga kafi ya fi magani.