Taron kasa: 'Ba za mu yarda da tazarce ba'

Image caption Wakilan arewan sun ce ba aikin taron ba ne ya samar da wani sabon kundin tsarin mulkin kasa

Wakilan arewa a taron kasa na Najeriya sun ce ba za su amince da daftarin tsarin mulkin da aka shigo da shi taron ba, saboda shiri ne na ganin Shugaba Jonathan ya yi tazarce.

A ranar Laraba ne wakilan babban taron kasar za su tattauna kan rahoton karshe na taron, wanda aka gabatar musu ranar litinin kuma aka ba su sa'o'i 24 domin su yi nazari a kansa.

Gabanin taron, wakilai daga arewacin kasar sun yi wata ganawa a tsakaninsu bayan da a ranar litinin suka ce ba za su amince da wani daftarin kundin tsarin mulkin da aka shigar cikin rahoton karshen ba.

Alhaji Sani Zoro daya daga cikin wakilan na arewa ya sheda wa BBC cewa daftarin yunkuri ne na tazarce ga Shugaba Jonathan.

Kuma ya ce duk wani kokari na tabbatar da daftarin tsarin mulkin zai iya kawo cikas ga taron baki dayansa.

Karin bayani