Dakarun Masar sun keta hakkin bil adama-HRW

Hakkin mallakar hoto na
Image caption Human Rights Watch ta bukaci a gurfanar da jami'an kasar Masar a gaban shari'a

Kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch, ta ce dakarun tsaron kasar Masar sun gudanar da kisan masu zanga zanga mafi girma a duniya.

Kungiyar ta ce sun aikata kisan ne a rana daya tak a cikin tarihi na baya bayan nan a cikin watan Ogustan bara.

A wani rahoto da ta fitar wanda ya yi cikakken bayani game da kisan magoya bayan hambararren Shugaban kasar Mohammed Morsi, ta ce akalla mutane 800 ne aka kashe a dandalin Rab na birnin Alkahira a ranar 14 ga watan Ogustan bara.

Human Rights Watch ta ce kisan da aka yiwa masu zanga-zanga fiye da 1,000 zai iya zama laifin cin zarafin bil adama, inda ta ce, adadin mutanen da aka kashe dai dai ya ke da wadanda aka hallaka a kisan kiyashin Tiananmen Square a kasar China.

Kungiyar ta Human Rights Watch ta kuma bukaci da a gurfanar da jami'an kasar Masar a gaban shari'a.