Masu kananan shekaru kan yi amfani da Facebook

Wata kotu a yankin arewacin Ireland ta umurci shafin sada zumunta na Facebook akan ya samar da bayanai akan yawan yara masu kankancin shekaru dake amfani da shafinsa .

Kotun ta kuma umurci Facebook akan ya samar da bayanai akan wata karamar yarinya da ta dinga magana da maza wadda kuma ta sa hotunanta da basu da ce ba a shafin.

Mahaifin yarinyar ne ya shigar da kara a gaban kotu , yana zargin kamfanin da sakaci da kuma rashin kare yancin diyyarsa.

Hakkin mallakar hoto FACEBOOK

Dokokin Facebook sun hana yara masu shekaru kasa da 13 amfani da shafin.

Sai dai lauyoyim mahaifin yarinyar sun ce tsarin yin rajista cikin sauki, ya ba yarinyar damar amfani da shafin tare kuma da jefa rayuwarta cikin hadari wajen haduwa da masu yin lalata da yara kanana.

Tun tana shekara 11, ta bude shafuka hudu inda ta saka hotunan da basu dace ba .

Ta kuma rika samun sakonin soyaya daga wurin maza sakamakon bayanan da ta sa a shafin Facebook.

Hakkin mallakar hoto THINKSTOCK

Sai dai an rufe shafinta bayan da kamfanin Facebook ya samu labarin abubuwan da ke faruwa.

Masu shigar da kara sun nemi kotun akan ta tilastawa Facebook ya samar da karin bayanai akan yawan yara masu kankanci shekaru dake amfani da shafin.

Sai dai a hukuncinsa, alkalin kotun ya nemi kamfanin akan ya samar da bayanai akan yawan yara masu kankanci shekaru da suka yi amfani da shafinsa daga shekarar 2011 zuwa shekarar 2014 a arewacin Ireland.