Google zai samar da intanet ta teku

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A 2016 ake sa ran wannan sabon layin sadarwar zai fara aiki.

Kamfanin Google da wasu jiga-jigan takwarorinsa guda biyar za su samar da wani layin sadarwa a karkashin tekun Pacific.

Za su yi hakan ne domin samar da wata dama da za ta kara inganta yadda intanet ke aiki cikin hanzari.

Wannan gammayya, za ta samar da hanyar hada Amurka da kasar Japan ta fannin sadarwar intanet, shirin da ake sa ran zai ci dala miliyan dari 300.

Idan an kammala shi, ana kuma sa ran zai iya bayar da damar aikawa da sama da fina-finan bidiyo 2,000 nau'in HD cikin dakika daya.

Kamfanonin da za su hada kai da Google din sun hada da China Mobile da China Telecom da Global Transit da KDD da kuma Sing Tel da dukkaninsu ke yankin Asia.

Layin sadarwar zai hada biranen Chikura da Shima da ke Japan da sauran manyan birane da ke yankin Kudancin Amurka irin su Los Angeles da San Francisco da Portland da kuma Seattle.

Ire iren wadanna layukan sadarwa da ake dasawa a karkashin Teku na taka muhimmiyar rawa wajen samar da hanyar sadawa ta intanet.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yankin tekun Pacific da za a shimfida wayoyin a cikinsa

A Shekarar 2008, an samu katsewar intanet tsakanin nahiyar Turai da Gabas ta Tsakiya da kuma yankin Asia bayan da aka katse layukan sadarwa a kusa da Alexandria da ke Masar.

Akalla kashi 65 cikin dari na hanyoyin sadarwar intanet din India ya samu tangarda a wannan lokaci.

A shekarar 2016 ake sa ran wannan sabon layin sadarwar zai fara aiki.