Ebola ta mamaye tsarin lafiyar Liberia

Maikatan kungiyar likitoci ta MSF na yi wa gawar mai Ebola feshin magani Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kalla mutanne 1,000 cutar ta hallaka, ya yin da wasu 1,800 suka kamu da cutar.

Ministan watsa labaran kasar Liberia ya amince cewa batun yaduwar cutar Ebola shi ne ya mamaye hukumar lafiya ta kasar.

Mr Lewis Brown ya shiadawa BBC cewa ayyuka sun yi matukar yawa a lokacin da cutar ta bullo, sai dai ya ce hukumomi na iya ka bakin kokarinsu domin tunkarar wannan matsala.

Mr Lewis ya kara da cewa barkewar cutar ta Ebola ta fi shafar Liberia, inda mutane suke zaune cikin zullumi da fargaba.

Ya kuma ce duk da cewa tsarin lafiyar Liberia ya fi kowanne rashin kyawu a duniya, amma ya musanta batun da ake yi na cewa hukuminin kasar ba su dauki matakan da suka dace ba akan cutar ta Ebola.

Ita ma kungiyar likito ta Medicins Sans Frontieress ta ce jami'a ba su yi tsammanin annobar za ta kai haka ba, dan haka tsarin kiwon lafiyar kasar ya gaza wajen shawo kan annobar.

Kusan mutane 1,000 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 1,800 suka kamu da cutar ta Ebola a yammacin Africa.

Barkeware cutar Ebola mafi muni da aka taba gani ta faro ne daga kasashen Liberia, da Saliyo da kuma Guinea, sannan kuma ta yadu a wasu kasashen cikin watanni.

Tun da fari jogorar kungiyar likitoci ta MSF a Liberia Lindis Hurum ta shaidawa BBC cewa wannan karon sun fadad ayyukansu fiye da yadda ake tsammani saboda barkewar cutar ta Ebola.

Lindis ta ce hakan ya biyo bayan rufe manyan asibitocin babban birnin kasar Liberia wato Monrovia har guda 5 na fiye da mako guda.

Ta kara da cewa a yanzu wasu asibitocin sun fara budewa, sai dai kuma wasu a bude suke amma babu jami'an lafiya a cikinsu.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Jmi'an lafiya na daga cikin wadanda cutar Ebola ta hallaka.

A ranar asabar din karshen makon da wuce ne masu zanga-zanga suka cika titunan kasar, su na cewa hukumomin kasar ba sa daukar gawawwakin wadanda suka kamu da cutar ta Ebola.

Ba da jimawa ba a ka girke dakarun soji a sassa daban-daban na kasar dan dawo da doka da oda, musamman a yankin da cutar ta fi kamari da kuma babban birnin kasar.

A bangare guda kuma kasar Guinea ta musanta rahotannin da ke cewa ta rufe iyakokin kasar da ta kasashen Liberia da kuma Saliyo.

Gidan talabijin din kasar sun bayyana cewa sanarwar farko da Ministan lafiyar kasar ya yi an yi ne bisa kuskure.

Hukumomin Guinea sun ce maimakon kulle iyakar kasar, an dai dauki matakai na lafiya ga duk wanda ke shiga ko fita iyakokin kasar.

Ita ma gwamnatin kasar Spain ta ce wani limamin Roman Katolika da ya kamu da cutar Ebola a Liberia za a gwada masa magungungunan da ba a taba gwadawa ga dan adam ba.

Sai dai Amurka ta yi amfani da su ga ma'aikatan agaji 'yan Amurka su biyu da suma suka kamu da cutar, wadanda kuma aka maida su gida dan yi musu magani, kuma an lura sun fara samun sauki.

Can a kasar Canada ma hukumomin kasar sun ce sakamakon binciken da aka gudanar akan wani maras lafiya da aka yi wa magani kusa da Toronto, wanda ya dawo kasar daga Nigeria ya na fama da mura da tari, ya nuna cewa baya dauke da kwayar cutar ta kabari kusa wato Ebola.

Ana dai daukar cutar ta Ebola ne idan wani ruwa na jikin mai dauke da cutar ya taba jikin wani, misali ta hanyar rungumar juna ko shan hannu dan gaisawa.

Kuma alamomin cutar dai sun hada da, Mura da ciwon kai, da kuma zazzabi, da amai da gudawa.

Kawo yanzu cutar Ebola bata da riga-kafi, ba kuma ta da magani.

Haka kuma cin naman daji ko Bush Meat a turance na janyo cutar ta Ebola.