Dattawan arewa sun soki gwamnati kan tsaro

Hare-haren Boko Haram a arewacin Nijeriya
Image caption Hare-haren Boko Haram a arewacin Nijeriya

Halin tashin hankali da yankin na arewacin Najeriya ya shiga na kai hare-hare dake lakume rayukkan jama'a ya sa kungiyar magabatan arewacin Najeriya mai suna elders forum ta kira wani taron manema labarai na duniya jiya a Kaduna.

A wajen taron 'yan jaridar, kungiyar ta bayyana takaici a bisa ci gaba da samun asarar rayuka a yankin arewacin kasar sanadiyyar hare-hare da ake ci gaba da kaiwa wadanda ake dangantawa da kungiyar nan mai tada kayar baya wato Boko Haram.

kungiyar na cewa tana mamakin ganin yadda duk da matsalar da ake ciki wasu manya na yankin ba su tabuka wani abin azo a gani ba wajen magance matsalar tsaro da kuma sauran matsalolin da arewa ke ciki.

Daya daga cikin 'ya'yan kungiya Barista Solomon Dalun ya bayyana cewar, ba su gamsu da kokarin da ake cewa ana yi na kawo karshen tada kayar baya a kasar ba.

Karin bayani