Ebola: Mutum na uku ya mutu a Nigeria

Kwayar cutar Ebola
Image caption Kwayar cutar Ebola

Hukumar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, watau ECOWAS ko CEDEAO, ta tabbatar da mutuwar wani jami'inta wanda shi ne mutum na uku da cutar Ebola ta hallaka a Najeriya.

Mutumin mai suna Jatto Asihu Abdulkadir, yana cikin wadanda suka taimaka wa ba-Amurken nan dan asalin kasar Liberia, Patrick Sawyer, lokacin da ya yanke jiki ya fadi sa'ilin da ya sauka a filin jirgin sama na Lagos.

Lamarin ya faru ne a watan da ya gabata kuma daga bisani Mista Sawyer ya mutu sakamakon kamuwa da cutar ta Ebola.

Daman a baya ma wata ma'aikaciyar jinya da ta kula da Mista Sawyer ta mutu, sakamakon kamuwa da ta yi da kwayar cutar, kuma wasu mutane da dama da suka kai wa mutumin dauki su ma sun harbu da cutar.

Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Canada ta ce za ta bai wa Hukumar Lafiya ta Duniya tallafin maganin gwaji na cutar Ebola domin taimakawa wajen yaki da annobar.

Cutar Ebola ta hallaka mutane sama da dubu daya a yankin Yammacin Afrika.