Ebola: Shugaba Jonathan na ganawa da gwamnoni

Image caption Bullar cutar Ebola a Najeriya ta jefa 'yan kasar cikin zullumi

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan na yin wata ganawa da gwamnonin jihohi da kwamishinonin lafiya a kan cutar Ebola.

Taron zai maida hankali ne kan matakan da suka dace a dauka domin kara dakile bazuwar cutar a kasar.

Hakan na zuwa ne bayan mutuwar mutum na uku kuma daya daga cikin wadanda suka taimaka wa dan Liberiyan nan Patrict Sawyer da ya kawo cutar Najeriya.

Tuni dai gwamnatin Najeriyar ta kafa wata cibiyar yaki da cutar da ke da zama a Lagos, wadda ke aiki ba dare ba rana wajen kauce wa cutar a kasar