Ebola: Nigeria na sa ido kan mutane 6 a Enugu

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Lokacin da ma'aikaciyar ta gudu ba ta da alamun cutar sai bayan da ta isa Enugu

Gwamnatin Nigeria ta ce a yanzu mutane shida ne kawai ta tabbatar sun yi mu'amala da wata ma'aikaciyar jinya da ke dauke da cutar Ebola a jihar Enugu.

Ministan lafiya na Najeriya, farfesa Onyebuchi Chukwu ya bayyana cewa an sallami mutane 15 bayan an tantance su an kuma tabbatar ba su yi mu'amala da ma'aikaciyar jinyar ba.

Ma'aikaciyar jinya dai ta sulale ne daga jihar Lagos, inda ake sa ido a kanta tare da sauran wadanda suka yi mu'amalar farko da dan Liberiyan nan Patrick Sawyer.

Ministan ya kara da cewa an yi amfani da motar daukar marasa lafiya na musamman domin maida matar da mijinta jihar ta Lagos.