Najeriya: An soke shirin horon Likitoci

Shugaba Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

Rahotanni daga Najeriya sun ce Shugaba Goodluck Jonathan ya amince da dakatar da tsarin horar da likitoci masu neman kwarewa.

Wata majiya a ma'aikatar lafiya ta kasar ta tabbatar wa BBC da faruwar hakan tana kwatanta matsayin likitocin a yanzu da matsayin dalibin da aka soke makarantar da yake karatu.

Rahotanni sun ce bayanin dakatarwar yana kunshe ne a wata sanarwa ta cikin gida daga babban sakataren ma'aikatar ta lafiya, Linus Awute, zuwa ga asibitocin gwamnatin tarayya.

A martaninsa shugaban kungiyar likitocin masu neman kwarewa ta kasa Dr Jubril Abdullahi yace matakin da shugaban kasar ya dauka bai dace ba.

Karin bayani