Manchester ya haramta amfani da kwamfuta

Kulob din Manchester United ya haramta wa magoya bayansa amfani da kwamfuta tafi da gidanka watau Tablet da laptops a filin wasansa .

Manchester United ya ce ya dauki wannan mataki ne sakamakon bayanan sirri da ya samu game da tsaro.

Ya kuma ce ya yi haka ne sakamakon sabbin kaidojin da aka fitar na hana amfani da kayan lataroni a filin saukar jiragen sama na Birtaniya.

Hakkin mallakar hoto PA

A cikin wata sanarwa da kulob din ya wallafa a cikin shafinsa na internet ya ce matakin zai shafi kanana da kuma manyan wayoyin tafi da gidanka

Kakakin Manchester United ya shaidawa BBC cewa sun dauki matakin ne bayan shawarar da aka bayar sai dai be bayana ko wanene ya ba su shawarar ba.

Sai dai ya ce matakin be shafi damuwar da wasu suka nuna akan masu amfani da kwamfuta tafi da gidanka wajen daukar hoto lokacin wasa inda a wasu lokutan su kan kare wasu masu kallo.

Sai dai kakakin Hukumar Primiya league ya ce ba su da alhaki game da matakin da kulob din Manchester ya dauka.

Hakkin mallakar hoto b

Haka kuma kakakin kungiyar Kwallon kafa ya ki ya ce uffam game da lamarin.

Sai dai abokan hammaya na Manchester watau Arsenal sun fitar da wata sanarwar inda suka ce kawo yanzu ba su sauya kaidojin buga kwallon kafa a filin wasansu ba .

Gwamnatin Birtaniya a watan yulin daya gabata ta yi shellar cewa fasinjojin da za su yi tafiya zuwa Amurka ko wadanda ke bin filin saukar jiragen sama na Birtaniya sai sun nuna sun kashe naurorin da ke cikin jakunansu

Matakin ya biyo bayan gargadin da jamian Amurka suka yi akan cewa sun sami bayanai masu sahihanci akan barazanar ta'adanci.