Taron kasa ya shure daftarin tsarin mulki

A Nigeria, wakilan babban taro na kasa sun amince da dukkan kudurorin da suka yi muhawara a kansu, bayan sun shafe kusan watanni biyar.

Taron wanda ya kawo karshe a ranar Alhamis ya yi watsi da wani daftarin sabon tsarin mulki wanda wasu suka yi zargin an shigar da shi ta bayan fage.

Wakilan taron sun amince cewa kudurorin da suka shafi kundin tsarin mulki za a mika wa Majalisar dokoki ta kasa domin ta yi gyara a kundin tsarin mulki na 1999 da ake amfani da shi yanzu a kasar.

Cikin batutuwan da suka ja hankali a lokacin zaman taron sun hada da batun rabon arzikin kasa da 'yan sandan jihohi da kuma soke kananan hukumomi.