Likitoci: Goodluck ya saba wa doka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Likitocin sun ce Shugaba Goodluck ya saba wa doka

A Najeriya, kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta yi watsi da matakin da shugaban kasar Goodluck, ya dauka na dakatar da tsarin horar da su, suka ce za su kalubalanci matakin.

Likitocin sun kuma ce game da yajin aikin da suke yi a kasar za su ci gaba domin mtakin ba zai karya musu guiwa ba.

A jiya ne dai babban sakataren ma'aikatar lafiya ta kasar, L.N. Awute ya aike da wata sanarwar dakatar da tsarin horarwar a asibitocin gwamnatin tarayya.

Hakan dai na nufin kimanin likitoci masu neman kwarewa 16,000 sun rasa aikinsu a asibitocin gwamnatin tarayyar Najeriyar.

Sanarwar ta gwamnatin Najeriya ta biyo bayan yajin aikin da likitoci ke yi a kasar ne, da kuma aka kasa cimma matsaya ta sasantawa tsawon lokaci.

Sai dai a tattaunawar da BBC ta yi da shugaban kungiyar likitoci masu neman kwarewar a Najeriyar, Dr Jibril Abdullahi, ya ce matakin da shugaban kasar ya dauka ya sabawa ka'ida, kuma za su dauki duk matakin da ya dace.

Shugaban kungiyar likitocin ya kuma zargi gwamnatin tarayyar kasar da yin abin da ta yi da nufin rarraba kawunan 'yan kungiyarsu.

Karin bayani