Saudi ta ba Majalisar Dinkin Duniya $100m

Sakatare Majalisar Dinkin Duniya Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mr Ban Ki Moon sakataren Majalisar Dinkin Duniya

Kasar Saudi Arabia ta bai wa Majalisar Dinkin Duniya dala miliyan 100 domin yaki da ta'addanci.

Da yake mika chakin kudin, jakadan Saudiyya a majalisar, Adel bin Ahmed Al-Jubeir, ya ce, ta'addanci abu ne da ya saba wa kowana addini, kuma annoba ce da ya wajaba kasashen duniya su hada hannu domin kawar da ita.

Za a yi amfani da kudin ne a cibiyar yaki da ta'addanci ta Majalisar Dinkin Duniyar, da aka kafa a shekarar 2011, bayan shirin da sarkin Saudiyyan, Abdullah ya kaddamar na yaki da ta'addanci.

Saudiyan ta bayar da kudin ne bayan, wata dala miliyan 500 da ta bayar domin tallafa wa 'yan gudun hijirar Iraqi, da ke guje wa hare- haren da masu da'awar jihadi ke kai wa a Iraqin.