'Yan Bindiga sun sace mutane 50 a Borno

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hare-haren Boko-Haram ya tashi kauyuka da garuruwa da dama a jihar Borno

A Nigeria, rahotanni daga garin Doron-Baga da ke jihar Borno na cewa 'yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun yi awon gaba da mata da maza da kuma kananan yara.

Wani basarake a garin ya shaida wa BBC cewa maharan sun sace fiye da mutane 50 a wani harin da suka kai a ranar Lahadin da ta gabata.

A cewar mazauna garin 'yan bindigar sun kashe mutane tare da jikkata wasu, haka kuma sun kona gidaje da dama.

Wata majiyar tsaro a Jihar Borno ta shaida wa BBC cewa jami'an tsaro sun samu labarin faruwar lamari mai kama da hakan, amma ta musanta cewa akwai wasu sojoji a wata makaranta wadanda suka zuba ido suna kallo lokacin da lamarin ya auku.

Har yanzu kungiyar na rike da 'yan mata 'yan makaranta sama da 200 da suka sace a garin Chibok a jihar ta Borno.