Likitoci sun bukaci gwamnati ta janye kora

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Liktocin sun shafe sama da wata guda suna yajin aiki

Kungiyar Likitoci ta Nigeria ta ce za ta ci gaba da yajin aiki har sai gwamnatin kasar ta janye sanarwar da ta ba da na korar Likitoci masu neman kwarewa kimanin dubu 16.

Haka kuma sai gwamnatin ta biya wa kungiyar ainihin bukatunta.

Sai dai kungiyar ta ce za ta ci gaba da bayar da gudunmawa a kokarin shawo kan bazuwar cutar Ebola da ta bulla a kasar.

A ranar Alhamis ne ma'aikatar lafiya ta kasar ta fitar da wani sanarwa wadda a ciki shugaba Goodluck Jonathan ya ce ya dakatar da horar da likitocin har sai abin da hali ya yi.