Ebola: Mutum na hudu ya mutu a Nigeria

Shugabar Hukumar Lafiya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugabar Hukumar lafiya Margareth

Ministna kiwon lafiya na Najeriya farfesa Onyebuchi Chukwu , ya ce ana kara tsaurara matakan dakile bazuwar cutar ebola bayan da aka samu mutum na hudu da ya hallaka daga cutar.

Ya ce "yanzu haka ana kula da mutane 177 a jihar Legas yayin da kuma da ake sa ido akan wasu mutane 21 a Enugu."

Ya zuwa yanzu dai cutar ta hallaka mutane 1,160, a kasashen da ta bayyana, lamarin da ya sa ta zama annoba mafi muni a tarihi, kuma hukumar lafiyar ta duniya na gargadi cewa har yanzu cutar na bazuwa.

Hukumar lafiya ta Duniya, WHO, ta ce da alamu ba a ma fahimci, ainahin girman annobar cutar Ebola da ta addabi, yankin yammacin Afrika ka ba, da hakan ya sa ake matukar takaita girmanta.

Hukumar ta ce, samar da bayanai kan wuraren da cutar ke yaduwa, abu ne mai muhimmanci, da zai taimaka kwarai, wajen tsara abin da ta kira matakai na musamman na yaki da annobar.