Ba a fahimci girman Ebola ba- WHO

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu fadakar da jama'a hanyoyin kamuwa da cutar Ebola

Hukumar lafiya ta Duniya WHO, ta ce da alamu ba a fahimci ainihin girman annobar cutar Ebola da ta addabi yankin Yammacin Afrika ba.

Hukumar ta ce hakan ya sa mutane da dama ke takaita girmar cutar wanda ke ci gaba da bazuwa a duniya.

WHO ta kara da cewa yana da matukar muhimmanci a rika samar da bayanai kan wuraren da cutar ke yaduwa don tsara matakai na musamman na yaki da annobar.

Ya zuwa yanzu dai cutar ta hallaka mutane 1,160, a kasashen da ta bulla, lamarin da ya sa ta zama annoba mafi muni a tarihi.