Boko Haram: 'Yan gudun hijira na kokawa

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption A Mubi 'yan gudun hijirar sun kai mutane dubu goma inji wani daga cikinsu

A Najeriya, 'yan gudun hijirar garin Gwoza da suke garuruwan Madagali da Mubi da kuma Askira Uba na cikin mawuyacin yanayi na rashin taimako saboda rashin tallafin hukumomi.

Al'ummar garin na Gwoza sun watse ne bayan hare-haren da 'yan boko haram suka kai musu inda suka kone fiye da rabin garin tare da kashe mutane da dama.

'Yan gudun hijrar dai sun roki gwamnati da ta kawo musu dauki bisa la'akari da halin da suke ciki.

Mutanen sun yi korafi cewa sama da mako daya da suka tsere har yanzu ba wanda ya kai musu taimako in ban da Sanata Ali Ndume da jama'ar Mubi daidaiku da suke tallafa musu.