Firai Ministan Iraki ya yi murabus

Nouri al Maliki Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Nouri al Maliki

Firaministan Iraqi , Nouri Al Maliki, ya sauka daga mukaminsa domin bayar da dama ga wanda aka zaba ya maye gurbinsa, Haider al-Abadi.

A jawabi da ya gabatar kai tsaye ta tashar talabijin din kasar, al-Maliki ya yi alkawarin bayar da goyon baya ga wanda zai gaje shi.

Ya ce "ina mai bayyanawa a gabanku cewa, domin aiwatar da tsare tsaren ci gaban siyasa da kuma kafa sabuwar gwamnati a kasar, ina sauka daga kan wannan mukami domin ba da dama ga dan uwana Dr Haidar Al - Abadi."

Jam'iyyar Al-Maliki ta 'yan Shia da Iran da kuma Amurka sun dauki Fraiministan a matsayin wani bangare na rikicin kasar, sun kuma dora alhakin dambarwar siyasar kasar a kan tsarinsa na aiwatar da manufofi da muradun Shia zalla.

Amurka dai ta jinjinawa Fira Ministan Al Malikin saboda matakin da ya dauka na sauka daga mukamin nasa.

Amurka dai ta jinjawa Nouri al Maliki akan matakin sauka daga mukaminsa da ya dauka